Nkurunziza zai saki prisononin siyasa
February 23, 2016Bayan ganawar magabatan biyu, Ban Ki-moon ya fadawa 'yan jarida cewar shugaba Pierre Nkurunziza kazalika ya tabbatar masa da kawo karshen matsin lamba da takunkumin da ke kan kafofin yada labaru , a kokarin gano bakin zaren warware rikicin wannan kasa ta Afirka, shekaru 10 bayan kawo karshen yakin batsatsa.
Tun daga watan Afrilu dai, sama da mutane 400 ne suka rasa rayukansu sakamakon tarzarce a karo na uku da Nkurunziza ya dage da nema. Yunkurin da ya jagoranci boren adawa daga jam'iyyun adawa, zaben da ya lashe, duk da cewar takarar tasa ta saba kundin tsarin mulkin kasar.
Tun a daren jiya ne dai babban sakaren majalisar Dunkin Duniyar ya gana da shugabannin jam'iyyun siyasar Burundin a babban birnin kasar ta Bujunbura, kafin ganawarsa da shugaban kasa a yau Talata.