Najeriya: Jam'iyyar NNPP na neman daukin ECOWAS
November 30, 2023NNPP dai na neman tsomin bakin na Majalisar ta Dinke Duniya da ma kungiyar kasashen ECOWAS. Magoya bayan jam'iyyar dai sun ce mai da kai zuwa ga duniyar na zaman hanya daya tilo ta neman adalci a cikin tsarin da ke neman komawa kana gani tana dada rudewa. Kowane lokaci cikin watan Disamban gobe ne dai ake sa ran kotun kollin za ta hukunci bisa shari'ar da ta dauki hankali cikin kasar kuma ke jawo muhawara bisa rawar alkalai. Ana dai kallon zanga-zangar da kila karkata zuwa ga duniyar ba sabon abu ne ba cikin batun siyasa ta kasar.
Zargin kotu da yin magudi a takkadamar ta mukamin gwamnan Kano
Hashim Sulaiman dai na zaman shugaban jam‘iyyar NNPP a Kano kuma ya ce sabo na salo. Barrister Abdul fage dai na zaman mashawarcin shari'ar jam'iyyar APC can a Kano, kuma ya ce masu kayan dadin na kara fitar da maita tsakar gari cikin tsarin da ba shi da mafita a zaurukan shari'a na kasar. Ko bayan Jihar Kanon alal ga misali can ma a Jihar Kogi dan takara na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jIhar ya ce ba shi da niyyar tafiya kotun bisa zargin komawar alkalan wata sabuwar jam'iyyar da ke hadaka da masu tsintsiya cikin harkokinta. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun siyasa ta kasar, ya ce dawowa daga rakiyar shari'ar na zaman barazana mai girma cikin siyasa ta kasar. Tuni hukumar kula da alkalai ta kasar ta ce tana shiri ta kaddamar da bincike cikin batun shari'ar ta Kano da nufin dauka na mataki a kokari na wankan tsarki cikin gidan alkalan.