1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya tattauna da Trump ta wayar tarho

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 9, 2016

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya taya sabon zababben shugaban kasar Donald Trump murnar zabensa.

https://p.dw.com/p/2SQFg
USA Wahlkampf Republikaner Donald Trump in Sarasota, Florida
Zababben shugaban Amirka Donald Trump Hoto: Getty Images/C. Somodevilla

A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, Trump da Obama sun amince cewa za su yi aiki tare, kamar yadda gidan talabijin din Amirkan na CNN ya ruwaito. Shi kuwa a nasa bangaren ministan harkokin kasashen ketare na kasar Iran da ke zamar abokiyar gabar Amirkan Mohammad Javad Zarif, ya nunar da cewa koda yake Iran ba ruwanta da harkokin cikin gida na wasu kasashe musamman ma Amirka, sai dai duk da haka yana fatan wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar zai ci gaba da amfani da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran din da kasashe shida masu karfin fada aji a dunyia kan makamashin nukiliyarta. A nasa bangaren shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan cewa ya yi:

 

"An bude sabon babi a Amirka, sakamkon yanke shawarar zaben Donald Trump da al'ummar kasar suka yi. Ina fatan zaben na Amirkawa zai haifar da natija mai kyau a bangaren dimokaradiya da 'yanci da kuma ci-gaba a wannan yankin namu. A madadina da al'ummar kasata ina yi wa Amirkawa fatan alkhairi a nan gaba." 

 

A watan Janairun shekara ta 2017 mai zuwa ne dai, Donald Trump zai shiga fadar White House a matsayin shugaban kasar Amirka na 45.