1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama: Ana bukatar wata hadaddiyar nahiyar Turai mai karfi

Mohammad Nasiru AwalApril 25, 2016

Duniya na bukatar wata nahiyar Tura mai karfi bayan ci gaban da aka samu na hadewar kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/1IcIR
Deutschland Barack Obama Rede in Hannover
Hoto: Reuters/K. Lamarque

A wani jawabi da ya yi a birnin Hannover a ranar ta biyu kuma ta karshe a ziyarar aikin da ya kawo a kasar Jamus, shugaban Amirka Barack Obama ya yi kira da nuna juriya don samar da abin da ya kira "wata hadaddiyar nahiyar Turai mai karfi". Ya ce duniya na bukatar wata nahiyar Turai mai karfi inda ya yi tuni da hadewar kasashen Turai da ya ce nahiyar ta samu gagarumin ci gaba a shekaru gommai da suka wuce. Saboda haka dole ne a kare muradun hadewar nahiyar daga masu adawa.

Da ya juya kan rikicin Siriya shugaban na Amirka ya yi kira ga kungiyoyin EU da NATO da su kara kwazo a rawar da suke takawa don kawo karshen rikice-rikice a Sirya da Iraki.

"Muna bukatar karin kasashe da za su ba da gudunmawa a farmakin da ake yi ta sama a Siriya da Iraki. Muna bukatar karin kasashe da za su ba da masu horo da za su taimaka wajen karfafa dakarun sa kai a Iraki. Muna kuma bukatar kasashe da za su ba da tallafin tattalin arziki a Iraki don daidaita al'amura a yankunan da aka 'yantar daga hannun kungiyar IS don hana masu matsanancin ra'ayin sake komawa yankunan."

A karshen ziyararsa a Jamus Obama zai gana da shugabannin EU da suka hada da Angela Merkel da Firaministan Birtaniya David Cameron da shugaban Faransa Francois Hollande da Firaministan Italiya Matteo Renzi a birnin Hannover, inda za su mayar da hankali kan matsalolin da suka yi wa duniya dabaibaye.