Obama: Zamu tallafa wa Kenya
July 25, 2015Shugaba Barack Obama ya bayyana Afirka a matsayin nahiya da ke samun sauyi . Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin bude taron koli kan bunkasa masana'antu a Kenya da ke zama tushensa a gabashin Afirka, taron kuma da kasar ta Amirka ta dauki nauyin tsara shi.
Shugaban ya ce Amirka za ta tallafa wa kasar ta Kenya wajen yaki da 'yan ta'adda daga kungiyar al-Shabab da ma wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.
Obama ya ce zaben shugaban kasa da aka yi a Burundi bai cika ka'idojin zabe ba saboda haka ya kamata a zauna kan teburin tattaunawa tsakanin 'yan adawa da bangaren gwamnati dan samun zaman lafiya a kasar.
Da yake jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya a ranar Asabar din nan a birnin Nairobi, Shugaba Obama ya bukaci a dena nuna wariyar jinsi a Afirka.
A yammacin ranar Lahadi ne dai ake saran shugaban ya bar kasar ta Kenya zuwa kasar Habasha.