Sudan za ta shiga tsakanin a rikicin Sudan ta Kudu
June 6, 2018Talla
Al Baschir ya ce a shirye yake ya kira wani taro da zai hada shugaba Salva Kiir da Riek Machar domin tattaunawa don yin sulhu. Wannan yunkuri na zuwa ne bayan da MDD ta gargadi sasan biyu da su samu famitar juna kafin nan da karshen wannan wata ko kuma majalisar ta dauki matakan hukuntasu. A shekara ta 2011 Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai kafin daga bisani a shekara ta 2013 kasar ta shiga yakin basasa. Sakamakon yadda shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon firaministansa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.