1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fuskanci tsananin zafi a Ostereliya

Zulaiha Abubakar
January 2, 2020

Mahukuntan kasar Ostireliya hadin gwiwa da hukumar agajin gaggawa, sun umarci dubunan 'yan yawon bude ido su gaggauta ficewa daga yankunan da ke makotaka da guraren da wutar daji ke ci a kasar cikin awanni 48.

https://p.dw.com/p/3VaPJ
BdT Satellitenbild vom Brand der Batemans Bay in Australia
Hoto: via Reuters

Wannan gargadi ya biyo bayan shirin ko ta kwanan da gwamnati ta yi don tunkarar tsananin zafi a karshen wannan mako da kasar zata fuskanta, kamar yadda hukumar kashe gobara ta yi hasashe. Ibtila'in gobarar dajin dai ya mamaye Kudu maso Gabashin kasar a ranar jajibirin sabuwar shekara al'amarin da ya haifar da ragaitar 'yan yawon bude ido.

 

Yanzu haka dai akalla mutane 18 sun rasa rayukansu sakamakon wannan gobarar daji. Da yake amsa tambayoyin manema labarai firaministan kasar Scott Morrison ya bayyana hadin kan al'umma a matsayin hanya guda ta kawo karshen yawaitar gobara a kasar, duk kuwa da cewar wasu daga cikin iyalan wadanda suka rasa rayuka a gobarar sun zargi gwamnati da rashin daukar matakan kare al'umma.