1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: An bayar da belin Imran Khan

May 13, 2023

Tsohon Firanministan Pakistan, Imran Khan ya isa gidansa da ke birnin Lahore bayan da wata kotu a Islamabad ta bayar da belinshi.

https://p.dw.com/p/4RIcL
Hoto: Anjum Naveed/AP/dpa/picture alliance

An dai sako jagoran 'yan adawan kasar ne bayan ya kwashe kwanaki a hannun jami'an 'yan sanda sakamakon zargin da ake masa na cin hanci da rashawa. A ranar Talatar da ta gabata ce, jami'an tsaro suke tsare Khan, lamarin da ya haifar da tarzoma a wasu sassan kasar tsakanin magoya bayansa da kuma jami'an tsaro, wanda hakan ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane kimanin 10 yayin da wasu daruruwa ciki har da jami'an 'yan sanda suka jikkata. Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda dubban magoya bayansa suka yi masa maraba tare da yin bikin sako jagoran nasu da yin wasanni da kade-kade da kuma raye-raye. Magoya bayan nasa da dama na kallo kamen a matsayin cinne na siyasa.