1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaPakistan

Gurbacewar muhalli a Punjab

Abdourahamane Hassane
November 6, 2024

Hukumomin lardin Punjab na Pakistan sun sha alwashin rufe makarantu,na kwalejoji da manyan makarantu har zuwa ranar 17 ga Nuwamba, sakamakon gurbacewar iska.

https://p.dw.com/p/4mhjV
Hoto: Rana Sajid Hussain/Pacific Press Agency/imago images

 Tuni dai lardin ya rufe makarantun firamare a babban birnin kasar, Lahore, a wannan makon tare da haramta gudanar da wasu harkoki na taruwar jama'a. Mako guda kenan da mazauna lardin miliyan 14 ke zaune cikin wani hali na hazo da turnikewar  hayaki mai gurbata muhalli. Punjab, da ke iyaka da Indiya, tana da mafi yawan manyan biranen kasar, inda kashi uku na mazaunan ba su kai shekaru  20.