1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin wa'adin beli ga tsohon firaminsta Imran Khan

Binta Aliyu Zurmi
September 12, 2022

Wata babbar kotu a kasar Pakistan ta tsawaita belin da aka ba wa tsohon firaministan kasar Imran Khan bisa zargin da ake masa da hannu a ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4Gjt0
Videostill | DW News | Imran Khan

Kotun da ta yi zamanta a wannan Litinin din ta tsawaita belin na Mr. Khan ya zuwa ranar 20 ga wannan wata na Satumba da muke ciki. Wannan kuma shi ne karo na hudu da kotu ke bashi wannan belin da tun da fari aka bashi kafin a kai ga tsare shi.

Khan wanda ya hallarci zaman kotun na ci gaba da tsayawa a kan matsayarsa na musanta zargin da ake masa na yin barazana ga jami'an tsaro da ma bangaren shari'a.

A watan Afirilun da ya gabata ne aka tunbuke Imran Khan daga madafun iko, wanda tun bayan nan yake gangami a sassan kasar daban-daban inda ake ganin yana zagon kasa ga gwamnatin Firaminista Shehbaz Sharif da kawancen jam'iyyun siyasar da ke mara masa baya.