1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta amince Indiya ta kafa sansanonin ba da agaji a yankin Kashmir

October 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvOJ
Pakistan ta amince da tayin da Indiya ta yi na kakkafa cibiyoyin ba da agaji ga wadanda bala´in mummunar girgizar kasar nan ya shafa a yankin Kashmir dake karakshin ikon Indiya din. Kamar yadda hukumomin kasashen biyu makwabtan juna suka nunar cibiyoyin zasu taimakawa wadanda suka tagayyara da abinci, ruwan sha, magunguna da kuma kayan sawa. Ana sa ran kafa cibiyoyin ba da agajin kafin ranar talata mai zuwa. A kuma halin da ake ciki MDD ta sake yin kira da a kaiwa yankunan dake fama da wannan bala´i dauki. Wakilan majalisar sun bayyana halin da ake ciki da cewa abin damuwa ne, musamman ganin cewa har yanzu ba´a samu sukunin kai kayan agaji ga daruruwan kauyuka dake kan tsaunuka ba. Ana fargabar cewa yawan wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar wadda ta auku a ranar 8 ga wannan wata na oktoba zai kai mutum dubu 80.