Pakistan ta kare kanta game da shirin ta na sayen iskar gas
January 26, 2006Shugaba Pervez Musharrafat na Pakistan, yace kokarin da kasar take na kulla yarjejeniyar sayan iskar gas daga kasar Iran, abu ne da bashi da wata dangantaka da kokarin da kasar ta Iran keyi na mallakar makamin nukiliya.
Musharrafa ya fadi hakan ne kuwa don kare wannan mataki da kasar ta Pakistan ke kokarin dauka, bisa Allah wadai da hakan da kasar Amurka tayi.
Musharraf ya kara da cewa batun sayen iskar gas din daga kasar ta Iran ta hanyar bututu, abu ne da bayan kasar ta Pakistan zai kuma amfani kasar India.
Shugaban kasar ta Pakistan wanda ya fadi hakan a lokacin da yake zantáwa da yan jaridu a can birnin Davos na kasar Switzerland, ya kuma tabbatar da cewa wannan mataki da kasar tasa ta dauka ba wane abu bane illa batu na inganta tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.