Pakistan ta nesanta kanta daga tukwicin kisa
September 23, 2012Gwamnatin Pakistan ta nesanta kanta daga tukwicin da wani minista a gwamnati ya yi alkawarin bayarwa ga dukkan wanda ya kashe mutumin da ya shirya fim din nan da ya yi batanci ga addinin musulunci. Wani mai magana da yawun Firaministan kasar Raja Pervez Ashraf yace babu ruwan gwamnatin da abin da ministan ya yi kuma ba manufa ce ta gwamnatin Pakistan ba. A ranar Asabar ce dai ministan sufurin jiragen kasa Ghulam Ahmed Bilour ya yi alkawarin bada tukwicin dala dubu 100 daga aljihunsa ga duk wanda ya kashe mutumin da ya shirya fim din nan da ya ci zarafin addinin musulunci da kuma manzon Allah, yana mai kira ga kungiyar Taliban dana Al-Ka'ida su shiga wannan muhimmin aiki na sadaukarwa.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu