Tsugune ba ta kare ba a siyasar Pakistan
May 24, 2023Talla
Karuwar tashe tashen hankula sun biyo bayan kama Imran Khan da hukumomi suka yi a farkon watan Mayu bisa zargin cin hanci da rashawa.
Ministan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ya baiyana wa 'yan jarida cewa tuni gwamnatin ta fara nazari kan wannan mataki saboda barazanar da jam'iyyar ke yi ga dorewar kasar wanda kuma ba za a lamunta da shi ba.
Shi dai tsohon Firaministan Imran Khan yana takun saka da gwamnatin Pakistan da kuma sojoji da suka mulki kasar kai tsaye ko kuma suka jagoranci gwamnatocin fara hula ta hanyar sa ido kan ayyukan su.