1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa

Binta Aliyu Zurmi
September 2, 2023

Daruruwan 'yan kasuwa a Pakistan sun fantsama a manya da kananan titunan kasar suna zanga-zangar yin Allah wadai da hali na matsin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.

https://p.dw.com/p/4VseY
Pakistan Zusammenstöße vor der Residenz von Imran Khan
Hoto: K.M. Chaudary/AP Photo/picture alliance/dpa

Masu boren na kokawa ne da tashin gwauron zabi da farashin man fetur ya yi da kuma karuwar kudin wutar lantarki da na ruwa gami da faduwar darajar rupee a kan dalar Amurka.

Tsohon sanata da ke shugabantar jam'iyyar Jammat-el-Islam, Sirajul Haq da ya kira wannan boren ya bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakan gaggawa na rage wa al'umma radadin halin matsin da suke ciki.

Birnin Karachi da ke zama cibiyar kasuwancin kasar da a baya ke cika makil da hada-hada, ya zama fayau sai ma kone-konen tayoyi da masu boren ke yi.