An kwantar da Fafaroma a asibiti
June 7, 2023Talla
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin shekara guda da za a yi wa Paparoma aikin tiyata, baya ga ta matsalar hanji da ya fuskanta a watan Yulin shekarar 2022.
Llikitocin da ke duba lafiyar Pararoma Francis mai shekaru 86 sun yanke shawarar sake yi masa tiyata a ciki bisa tsananin ciwon da yake fama da shi.
Sai dai fadar Paparoman ba ta bayyana ko zai soke tafiye-tafiyen da zai yi nan gaba kamar yadda ya wakana a bara ba.
A baya Paparoma Francis ya bayyana cewar a shekarar 2021 ya taba ganin likitan kwakwalwa a kasarsa ta haihuwa Ajantina a lokacin da yake dan matashi, domin taimaka masa wajen magance matsalar damuwa da ta samo asali daga mulkin kama-karya na soja.