1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma Francis: Kawo karshen rikicin Isra'ila da Hamas

Binta Aliyu Zurmi
October 29, 2023

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi kira ga bangarorin da ke fada da juna a yankin Gabas ta Tsakiya wato Isra'ila da Hamas da su kai zuciya nesa don kauce wa ci gaba da zubar da jinin fararen hula.

https://p.dw.com/p/4YAXG
Italien | Welt-Bischofssynode in Rom
Hoto: Andrew Medichini/AP Photo/picture alliance

A jawabinsa yayin addua a majami'ar St. Peters da ke Vatican, Paparoma Francis ya kuma bukaci kungiyar Hamas da ta saki mutanen da take ci gaba da garkuwa da su bayan mummunan harin da ta kai wa Isra'ila.

Wannan bukata na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta bukaci mazauna yankunan zirin Gaza da su koma kudanci domin samun kayayakin agaji. 

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar dubban Falasdinawa ne suka fasa dakunnan ajiyar kayayyakin agaji da ke Gaza, inda suka kwashi fulawa da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.

Makwanni 3 ke nan aka kwashe ana dauki ba dadi tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da ramuwar gayya a harin da Hamas ta kai mata wanda ya yi sanadiyar rayukan 'yan Isr'ila 1400.