1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman gafara kan lalata a Ireland

Gazali Abdou Tasawa
August 26, 2018

Paparoma Francis shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya ya nemi gafara Ubangiji kan aikata lalata da limaman coci suka yi a kasar Ireland.

https://p.dw.com/p/33oJ4
Irland Besuch Papst Franziskus
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Dunham

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya, Paparoma Francis ya nemi gafarar Ubangiji kan batun badakalar lalata da mata da yara da aka bankado limaman cocin Katolika sun aikata a kasar Ireland. Ya nemi wannan afuwa a lokacin da yake ziyartar a wannan Lahadi babbar cocin birnin Knock da ke a nisan kilo-mita 180 da birnin Dublin inda ya samu tarba daga mabiya sama da dubu 45.

Daga shekara ta 2002 ya zuwa yanzu mutane sama da dubu 14 da 500 ne suka sanar da cewa limaman cocin kasar ta Ireland sun cin zarafinsu ta hanyar neman yin lalata da su ko kuma aikatawa baki daya. Kuma an zargi shugabannin cocin Katolika na kasar ta Ireland da bayar da kariya da daruruwan limanan cocin da suka aikata wannan danyan aiki.

Kazalika wasu ayyukan bincike sun bankado yadda gwamnatin kasar ta Ireland tare da hadin bakin coci-coci na kasar ke bayar da ba ta hanyar ka'ida ba rikon yaran da matan suka haifa bayan latatar.