1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Paparoma ya yi na'am da shugabancin mata a Vatican

March 19, 2022

Kafin yanzu dai maza ne ke mamaye galibin manyan mukaman fadar ta Vatican. Sai dai sabon kundin da Paparoma ya fitar mai shafuka 54, ya cire maganar jinsi daga cikin sharudan samun mukami a darikar ta Katolika.

https://p.dw.com/p/48jkN
Italien Vatikan Papst hält Neujahresmesse
Hoto: Guglielmo Mangiapane/REUTERS

Paparoma Francis ya fitar da sabon kundin tafiyar da fadarsa ta Vatican ta Kiristoci mabiya darikar Katolika. Sabon kundin da aka fitar a wannan Asabar mai suna Curia, ya zayyana cewa duk wani mabiyin darikar da ya mallaki wasu shaidun kammala karatunsa na Kiristanci, namiji ko mace, zai iya samun mukami a fadar ta Vatican da ke kasar Italiya. 

Shekaru tara aka kwashe dai ana tsara sabbin dokokin da ake sa ran za su fara aiki daga ranar 5 ga watan Yunin wannan shekara da muke ciki.