1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya fara raha bayan tiiyatar hanji

Mouhamadou Awal Balarabe
June 8, 2023

Shugaban darikar Katolika ta duniya ya jure wa tiyatar sa'o'i uku da likitoci suka yi masa a birnin Rome sakamakon matsalar hanji da yake fama da ita. Sai dai Paparoma zai ci gaba da murmurewa har zuwa 18 ga watani Yuni.

https://p.dw.com/p/4SKML
Paparoma FrancisHoto: Riccardo De Luca/Anadolu Agency/picture-alliance/dpa

Likitan da ya yi wa Paparoma Francis tiyata ya ce aikin gaggawa da aka yi masa a hanji a wani asibiti da ke Rome babban birnin kasar Italiya ya gudana ba tare da wata matsala ba. Shugaban darikar Katolika ta duniya ya shafe kusan sa'o'i uku ana yi masa tiyata, amma tuni ya fara raha, in ji jami'an kiwon lafiya.

Paparoma Francis mai shekaru 86 da haihuwa na fama da matsalar toshewar hanji da ta sa aka fara yi masa aiki watanni 11 da suka gabata. Tuni ma fadar Vatican ta soke duk wasu tafiye- tafiye da manyan ayyukan ibada da Paparoma ya kamata ya yi har zuwa 18 ga Yuni.