Paparoma ya yi kira ga matasan kasar Kuba da su hada kai
September 21, 2015A ci gaba da ziyarar da yake kai wa kasar Kuba Paparoma Francis ya yi kira ga matasan kasar da kar su bari a yaudaresu da wasu akidoji da za su zamesu wani tarnaki kan muradunsu na neman cigaba. Paparoma ya yi wannan kira ne lokacin ganawarsa da wasu daruruwan matasa a Havana babban birnin kasar ta Kuba. Da farko ya gana tsawon mintuna 30 da jagoran juyin juya hali kuma tsohon shugaban Kuba Fidel Castro a gidansa, inda suka tattauna kan batutuwan da suka hada da kare muhalli da dai sauransu. Daga bisani sun yi musayar littattafai tsakaninsu. A kuma halin da ake ciki Paparoma Francis ya isa Holguin da ke zama birni na uku mafi girma da ke a gabashin kasar, inda tuni dubun dubatan mutane suka yi cincirindo a dandalin da Paparoman zai jagorancin sujjada ta wannan rana.