Limamin cocin Katolika ya gana da jagoran Shi'a a Iraqi
March 6, 2021A yayin ziyarar da Paparoma Francis din ya kai wa al-Sistani a garin Najaf da ke Iraqin, al-Sistani ya ce ya kamata Kiristoci su yi rayuwarsu kamar yadda kowane dan Iraqi yake da 'yancin yin walwala a kasar.
Paparoma Francis din ya gode wa jagoran Shi'an na Iraqi, a kokarin da yake yi na ganin an kare rayukan tsiraru da ake gallaza wa a cikin al'umma.
A baya dai akwai kimanin Kiristoci kusan miliyan daya a Iraqi, amma tun bayan kutsawar da Amirka ta yi a kasar a shekara ta 2003 da kuma rikice-rikicen addinin da suka biyo bayan hakan, sai yawan Kiristocin yanzu ya koma tsakanin 250,000 zuwa 400,000.
Limamin cocin Katolikan dai na ziyarar kwanaki hudu ne a Iraqi a wani mataki na samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin Kiristoci da Musulman kasar.