1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma zai gana da tawagar musulmi a birnin Rome

September 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuiJ

Paparoma Benedict na 16 zai gana da tawagar jakadun ƙasshen musulmi a gidan sa dake kusa da birnin Rome. Ganawar na da nufin ɗinke ɓaraka tsakanin mujamiár Rome ta Cocin katolika da kuma alúmar musulmi, bayan kalaman da Paparoman ya yi a baya bayan nan wanda ya harzuƙa musulmi a faɗin duniya. Jakadu daga ƙasashen Iran da Turkiya da Morocco sun baiyana aniyar su ta halartar taron. Zanga zanga ta ɓarke a ƙasashen musulmi da dama bayan wata lacca da Paparoman ya gabatar a ranar 12 ga watan Satumba yayin wata ziyara da ya kawo nan Jamus inda ya ruwaito jawaban wani basarake na ƙarni na goma sha hudu wanda ya baiyana wasu daga cikin koyarwar Manzo Annabi Muhammad da cewa Mugun nufi ne kuma bai dace da aƙidar dan Adam ba. Tuni dai paparoman ya baiyana nadama a game da waɗannan kalamai.