1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na son kotu ta dawo mata da kujerunta a Filato

Ubale Musa AMA(MAB)
January 15, 2024

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ta bukaci kotun kolin kasar da ta sake nazarin shari'un 'yan majalisun tarraya da na jihohi a Filato.

https://p.dw.com/p/4bFyP
Atiku Abubakar dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023
Atiku Abubakar dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023 Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Ya zuwa yanzu daukacin kujerun jam'iyyar PDP 16 dake zauren majalisar dokokin jihar Filato sun koma APC, ko bayan 'yan majalisar dattawa guda uku wakilan jam'iyyar adawar da suka suka suaya sheka zuwa APC, duk a albarkacin wani hukuncin kotun daukaka kara a kotun kolin da ke Abuja.

Tuni uwar jam'iyyar ta PDP ta kasa ta isa kotun koli da nufin neman sake duba daukacin hukuncin kotun daukaka karar da nufin a mayar mata da kujerun dake da tasiri a mulki na jihar.

Karin Bayani :  'Yan adawar Najeriya na kokarin yakar APC

Sashe na 285 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi dakatar da sauraron shari'un 'yan majalisun kasar a gaban kotun daukaka kara , kana a cewar Barrister Buhari Yusuf dake zaman wani lauyan mai zaman kansa a Abuja, "Bakin alkalamin shari‘un tuni ya riga ya bushe." 

'Yan majalisun dokokin jihar Filato daga jam'iyyar PDP na fuskantar rashin goyon baya na sauran 'yan majalisu daga bangaren jam'iyyar adawa.

Karin Bayani : Rikicin siyasar jihar Rivers ya dauki sabon salo

Rikicin 'yan majalisun dokoki a jihohin Najeriya ba sabon abu ba ne a fagen siyasar kasar, matakin da ya haddasa gwamnoni da dama rasa kujerunsu.