Pele: Hotunan gwarzon kwallon kafa
Edson Arantes do Nascimento, da aka fi sani da Pele, ya kasance dan wasan kwallon kafa mafi shahara a duniya. Mun yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman tarihin rayuwar gwarzon dan kasar Brazil din cikin hotuna na.
Kungiyar FC Santos
Kungiyar FC Santos ita ce kungiyar farko da Pele ya soma taka wa leda, tun ya na dan shekara 15 ya soma taka leda a kungiyar. Baya ga cikin gida Brazil kungiyar FC Santos ta shahara, inda take fita tana karawa da kungiyoyi a kasashen Turai da Amirka. Nan hoton Pele ne, a yayin wani wasan sada zumunta tsakanin FC Santos da Washington Darts a shekara ta 1970.
Gasar cin kofin duniya
Duniya ta san Pele sakamakon bajintarsa, a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a kasar Sweden a shekara ta 1958. Karon farko da ya je gasar cin kofin duniya kenan, a lokacin yana da shekaru 17. Pele ya zura kwallaye shida, a wasanni hudu da ya buga a gasar. Shi ya ci kwallon da ta bai wa Brazil nasara kan Faransa, a wasan kusa da na karshe wato semifinals.
Basira da bajinta
Pele ya dauki kwallon kafa a matsayin abu mai muhimmanci da ke so, kuma a kan hakan ya gina salon takun ledarsa. Yana da bajinta da hazaka da kuma baiwar gudu da dabaru da suka sa ya sha gaban takwarorinsa. Ya shahara sosai saboda salon murza leda da yadda ya ke iya zura kwallo a raga ta kowanne hali. Wannan hoton na nuna bajintarsa wajen zura kwallo a raga, yayin wani wasa a shekara ta 1968.
Shekara ta 1966
Bayan nasarar lashe kofin duniya har sau biyu a jere a Sweden da Chile, Brazil ta isa gasar cin kofin kwallon kafa a Ingila da burin sake lashe kofin. Pele ya zura kwallo guda a karawar Brazil da Bulgariya, wanda ya sanya shi zama dan wasan da ya zura kwallaye a gasa uku a jere. Sai dai Brazil ta fice daga gasar tun a zagayen farko, sakamakon mugun taku na 'yan wasan Potugal da Bulgariya.
Nasara a gasar duniya karo na uku
Gasar shekara ta 1970 ta kasance gasarsa ta karshe da ya wanye cikin yanayi na farin ciki, sakamakon yadda Brazil ta yi nasarar doke Italiya da ci hudu da daya a zagayen karshe. An gudanar da wasan na karshe, a filin wasa na Azteca da ke kasar Mexiko. Pele ya ci wa kasarsa kwallaye hudu a gasar tare da lashe kyautar takalmin zinare da ake bai wa dan wasan da ya fi saura bajinta.
"Tchau Selecao"
Pele ya yi wasansa karo na 97 kuma na karshe ga kasarsa Brazil, a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1971. Magoya bayansa sama da dubu 100 ne suka yi cin-cirindo a filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Janeiro domin kallon fafatwar da Brazil da Yugoslavia suka yi, inda suka tashi da ci uku da uku. A lokacin yana da shekaru 30, ya dai ci gaba da taka leda a matsayin sana'a a kungiyar Santos.
Birnin New York
Bayan kamalla kakar wasa a shekarar 1974, Pele ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa. Sai dai bayan shekara guda ya kuma sanar wa duniya cewa, zai koma taka leda a kungiyar New York Cosmos da ke arewacin Amirka. Ya ce burinsa shi ne, ya bunkasa wasan kwallo a kasar da kwallon hannu da na zari ruga suka fi yin suna. Ya jagoranci Cosmos a lashe kofin gasar da aka gudanar, a shekara ta 1977.
Bankwanan karshe
Pele ya karkare sana'arsa ta murza leda a kungiyar Cosmos da wata fafatawa da suka yi da tsohuwar kungiyarsa FC Santos, a filin wasa na Giants a ranar daya ga watan Oktobar shekara ta 1977. Wadanda ke cikin wannan hoton sun hada da gwarzon dan kwallon kafar Jamus Franz Beckenbauer (na hudu daga dama) da Carlos Alberto (na uku daga dama) da kuma shahararren dan damben zamani marigayi Muhammad Ali.
Shahararrun 'yan fina-finai
A shekara ta 1981 Pele ya shiga harkar fina-finai, inda ya fito a wani shiri mai suna Escape to Victory. Shiri ne kan rayuwar wasu fursunoni da yadda suka hada tawaga, a wata gasa da suka fafata da 'yan Nazi da ke tsare da su. Pele ya fito a cikin shirin tare da shahararru a harkar fina-finai na masana'antar Hollywood, waadan da suka hadar da Michael Caine da Sylvester Stallone.
Pele a matsayin ministan wasannin Brazil
Pele ya samu tayin aiki daga sassan duniya bayan ya yi ritaya, a shekarar 1994 ya zama jakadan UNESCO. Shekara guda bayan nan, shugaban kasar Brazil na wancan lokacin Fernando Henrique Cardoso ya nada shi ministan wasanni. Pele ya samar da kudurin da ya yaki matsalar cin hanci da ta dabaibaye hukumar kwallon kafar kasar, kudirin da ake kira da "The Pele law."
Pele da dansa Edinho
Pele ya auri mata akalla uku, yana kuma da yara da ya haifa tare da matan da ya aura da ma wadanda bai aura ba. Daya daga cikin 'ya'yansa shi ne, Edinho wanda ya bi sahunsa na zama mai tsaron raga. Sai dai Edinho ya fada hannun hukuma bayan samun shi da laifin halasta kudin haram da safarar miyagun kwayoyi, an garkameshi a gidan yari na tsawon lokaci.
Rashin lafiya
Pele ya fara rashin lafiya. A shekara ta 2012 an yi masa aiki a kugunsa, inda ya koma amfani da keken masu bukata ta musanman. Ko a wannan hoton da ya halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Rasha, a shekara ta 2018. Ga shi tare da shugaban Rashan Vladimir Putin da gwarzon kwallon, marigayi Diego Maradona. Wata guda bayan nan, aka yi masa aiki na cire masa duwatsu daga cikin kodarsa.