Pentagon ta ce a shirye take ta afka wa Siriya
August 25, 2013Talla
Sakataren tsaron Amirkan Chuck Hagel ne ya bayyana hakan a wannan Lahadin a birnin Kuala Lumpur lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, inda ya ce sojin ruwansu da ke yankin Meditarrenean na cikin shirin ko ta kwana dangane da wannan batun.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da yin kace na ce game da amfani da makamai masu guba a yakin Siriyan wanda bangaren gwamnati da na 'yan adawa ke zargin juna a kai.
A ranar Asabar babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan kawar da makamai ta isa Siriyan don yin matsin lamba ga gwamnati Basha al-Assad da bar masu sa ido na Majalisar ta Dinki Duniya su gudanar da bincike don hakikance gaskiyar lamarin.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal