Pyongyang: Amirka na takalarmu da yaki
September 26, 2017Talla
A wata hira da ya yi da 'yan jarida a birnin New York, ministan harakokin wajen koriya ta Arewa Ri Yong Ho ya ce tunda dai har Amirka ta yi wa kasarsu tayin yaki to kuwa kasar tasu na da izinin daukar matakan kare kanta da suka hada da kakkabo jiragen yakin kasar ta Amirka masu zuwa shawagi ko da kuwa ba su shiga sararin samaniyar Koriya ta Arewar din ba.
Sai dai kakakin gwamnatin kasar ta Amirka Sarah Huckabee-Sanders ta ce wannan zargi ba shi da tushe domin kuwa babu inda Amirka ta ayyana wani yaki. Daga nata bangare Koriya ta Kudu ta yi kira ga kawarta ta Amirka da ta daina biya duk wata takula da Pyongyang ke yi mu su da kaucewa duk wani rikicin soja wanda na iya rikidewa zuwa abin da ba a san shi ba.