Koriya ta Arewa: Trump ya saba alkawari
May 25, 2018Ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta ce matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na soke ganawar karya alkawari ne, kuma bai cimma burin sauran kasashen duniya ba. Amma dai gwamnatin Pyongyang a shirye ta ke a ko wani lokaci domin sake shiga tattaunawar. Trump ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan martanin Koriya ta Arewa kan kalaman matakin da Amirka za ta iya dauka kan Koriya ta Arewa idan ta ci gaba da cijewa kan sarrafa makaman nukiliya, Trump ya ce soke haduwar shi ne matakin da yafi dacewa da kasashen biyu. Soke ganawar dai na zuwa ne jim kadan bayan da Koriya ta Arewa ta sanar da rusa cibiyar gwajin makaman nukiliyarta, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana takaicin rashin cika alkawarin ganawa shugabannin biyu da aka dade ana jira.