Pääbo ya samu Nobel ta fannin likitanci
October 3, 2022Talla
Wannan likita Svante Pääbo mai shekara 67 a duniya da ke da zama a tarayyar Jamus, ya kaddamar da gwaje-gwajen kwayoyin hallitar bil'Adama shekaru 13 da suka gabata masu nasaba da tushen mutum fiye da shekaru dubu 30, kana ya gano cewa asalin gangar jikin dan Adam yana kunshe da sanadarin da ke ba wa garkuwar jiki kwarin gwiwar jajircewa wasu cututuka.
Svante Pääbo dai, shi ne kwararren likita na 113 da ya samu kyautar Nobel a tarihi, a daura da wasu masana 226 da suka kunshi masu bincike kan fannoni da suka jibanci bani Adama ciki har da mata 12.