1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi na cin karo da juna kan zaben jihar Osun

Ubale Musa M. Ahiwa
July 18, 2022

Sa'o'i bayan kammala zaben gwamnan jihar Osun na kudancin Najeriya, ra'ayi na bambanta game da sakamakon zaben da wasu ke ganin zakaran gwajin dafi ne ga babban zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4EITk
Nigeria Wahlen l Wähler gibt Stimme ab, Lagos
Hoto: Stefan Heunis/AFP

Kama daga sata ta akwatun zabe ya zuwa ga shi kansa rinto na kujerar dai, zargi na magudi cikin harkar zabe dai na da dadadden tarihin da ke kusan kankankan da batun zaben a cikin Tarrayar Najeriya. To sai dai kuma zabuka guda biyu na gwwamnoni a jihohin Ekiti da Osun da suka gudana a karkashin sabuwar dokar zabe ta kasar dai na nuna alamun bambanta ko dai ga yawa na korafin a bangaren masu siyasa, ko kuma rage zargin tayar da hankali da  kokarin murde zaben.

Duk da cewar dai an dauki lokaci ana tafkawa a tsakanin 'yan majalisar tarrayar da bangaren zartarwa kafin iya kaiwa ga amincewa bisa dokar dai, sakamakon da ya fito daga jihohin guda biyu dai ya kwantar da hankula na da dama a cikin Najeriyar a halin yanzu. Dokar dai ta tanaji ayyana sakamakon tun daga rumfar zaben ko bayan aike da shi ta kai tsaye ta injuna masu kwakwalwaya zuwa cibiya ta tattara sakamakonsa, abun kuma da ya kare tasiri na akwatin zabe, balle kuma jibge kuri'un bogi da kila ma sauyi na sakamakon da ke kasa.

Nigeria l Wahlurne, Junge Wählerin gibt ihre Stimme ab
Hoto: picture alliance / NurPhoto

Sabon tsarin dai daga dukkan alamu na zaman na kan gaba cikin jerin sabon yanayin da kasar take gani a halin yanzu a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai taka rawa a cikin harkokin zabe a kasar. To sai dai kuma in har ana shirin kai karshen sata ta Akwatu, daga dukkan alamu dai akwai  sauran aiki a kokarin kasar na isa tsaftar zabe. Shehu Musa Gabam dai shi ne shugaban jam'iyyar SDP na kasa, jam'iyyar da ta zo ta biyu can a jihar Ekiti, ta kuma taka rawa mai tasiri a jihar Osun, kuma ya ce da akwai bambanci cikin jihohin guda biyu.

Amma kuma koma wane tasiri fasahar take shirin ta yi a kokari na kaiwa ya zuwa samun daidai, ba dai a yabon dan kuturu, a fadar Barrista Mohammed Tudun wada da ke kallon zabe cikin kasar na lokaci mai nisa, a cikin al'adar ko mutuwa ko yin rai da ta dauki lokaci tana tasiri a cikin Najeriyar.

Tarrayar Najeriya dai na  a tsakanin ingantar tsarin zaben da nufin kauce wa rigingimu na siyasar da suke daukar fasalin addini da kabila, kuma ke iya kaiwa ya zuwa barazana mai girma, ko kuma ci gaba a cikin tsohuwar al'adar da ke iya kaiwa ga fasa kowa ya rasa cikin fage na siyasa ta kasar.