1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2018

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sanar da cewa shugaban kasar Salva Kiir da jagoran 'yan adawa Riek Machar sun amince su raba madafun iko a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/325Ap
Südsudan Präsident Salva Kiir und Vizepräsident Riek Machar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Wannan dai na zaman wani mataki na baya-bayan nan da ka iya kawo karshen rikicin kasar da ya rikide zuwa yakin basasa na tsahon shekaru. Ministan yada labaran kasar Michael Makuei Lueth ne ya sanar da hakan a Khartoum babban birnin kasar Sudan. A nasan bangaren ministan harkokin kasashen waje na Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed ya bayyana cewa za a sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu ta karshe a ranar biyar ga watan Agusta mai zuwa. Kamfanin dillancin labaran Sudan din da a yanzu haka ke zaman kasar da ke jagorantar tattaunawar sulhun, SUNA ya ruwaito cewa Shugaba Kiir zai kasance shugaban kasa har zuwa lokacin da za a mika mulki ga sabuwar gwamnati, yayin da Machar zai rike matsayin mataimakin shugaban kasa na farko. Tun dai a watan Disambar shekara ta 2013 ne rikici ya barke a 'yar jaririyar kasar ta duniya Sudan ta Kudu, tsakanin magoya bayan Shugaba Kiir da kuma Machar da ke zaman mataimakinsa a wancan lokaci, rikicin da ya rikide ya zama yakin basasar da ya haddasa asarar rayuka tare da tilasta wasu miliyoyi yin gudun hijira zuwa kasashe makwabta, yayin da wasu kuma ke fama da matsalar rashin abinci.