Rahotan Unicef kan karancin ruwan sha da muhalli mai tsabta.
September 28, 2006Acikin rahotan data gabatar ayau,asusun lura da yara kanana ta mdd watau UNICEF,ta bayyana cewa akwai kimanin mutane Billion 2.6 a duniya,akasarinsu a nahoyoyin Afrika da Asia dake fama da karancin kayayyakin da ake bukata na tsabbatace muhalli,wanda ke haddasa illar kamuwa da cutar gudawa da sauran cututtuka dake da lahani wa yara.
Unicef tace a wani bincike data gudanar kann ruwansha da tsabtace muhalli a kasashe masu tasowa,na nuni dacewa zaa iya cimma burin mdd a dangane da samar da ingantaccen ruwan sha musamman a birane,sai dai bazaa iya cimma burin samarda dakunan ba haya ba kamar yadda ake bukata.
Rahotan dai yayi nazari ne adangane da binciken harkokin ruwan sha mai kyau,da da muhalli mai tsabta daga shekarata 1990 zuwa 2004,inda ta bada misalin kasashen zasu iya cimma burin da mdd ta sanya a gaba,wanda aka cimma a shekarata 2000.
Rahotan yace nanda shekara ta 2015,rabin alummomin kasashen duniya ne zasu wadatu da ruwan sha mai tsabta,da muhalli mai tabta.Directar gudanarwa ta Unicef,kuma tsohuwar sakatariyar harkokin gona ta Amurka,Anne Veneman tace duka da cigaba da aka samu wanda kuma abun yabawa ne,akwai kimanin yara kanan million 425,da suke kasa da shekaru 18,wadanda basu da sukunin samun ingantaccen ruwan sha,ayayinda akwai yara million 980 dake fama da karancin muhalli mai tabta.
Baki daya dai akwai kimanin mutane billion 1.2,ko kuma karin kashi 78 da cikin 100 a shekarata 1990,zuwa kashi 83 daga cikin 100 a shekarata 2004,da ke samun ruwan sha mai tsabta,wanda kuma zai cimma burin mdd na shekarata 2015.
To sai har yanzu akwai sama da mutane billion 1 dake fama da karancin ruwan sha a 2004 daga daga wuraren da suke debo ruwan,kamar koguna da rijiyoyi,kuma bisa dukkan alamu zaa samu kawar wadanda ke fama da wannan matsalar ,inji rahotan.Wannan matsala dai tafi yin tsamari ne a yankunan sahara na Afrika,yankin dake wakiltar kashi 11 daga cikin 100 ,na yawan adadin mutanen dake doron kasa,kuma kusan kowane mutun guda daga cikin uku na wadannan yankuna na fama da karancin ruwan sha mai tsabta.
To sai dai Rahotan UNICEF din yayi nuni dacewa,ana kuma fama da rashin ingantaccen ruwan sha a kasashen arewacin Afrika da yankin gabas ta tsakiya.A kasashe kamar Djibouti da Iraki da Morokko ,alal misalisama da kashi 40 daga cikin 100 na mazauna yankunan karkararsu ke fama da karancin ruwan sha.
Rahotan yace wannan matala ta karan cin ruwa da muhalli mai tsabta yafi muni a kasashe kamar Nigeria da Janhuriyar democradiyyar Congo da Niger da Equitorial Guinea da Tchadi.
A halin da ake ciki yanzu,inji rahotan dai an samu karuwan wuraren ban daki irin na zamani zuwa kashi 59 daga cikin 100 a 1990,amma sai dai har yanzu hakan ya gaza cimma burin mdd.
Daga cikin kimanin mutane billion2.6 dake fama da karancin ruwan sha da muhalli mai tsabta a duniya baki daya,billion 2 daga cikin su mazauna ne a yankunan karkara,kana daga wannan adadi kashi biyu daga cikin uku na nahiyar Afrika,ayayinda kashi 37 daga cikin 100 na daga yankin kudancin Asia.