Rahoton Bankin Duniya da Asusun IMFakan manufofin raya kasa
April 13, 2005Abin farin ciki guda daya dake kunshe a rahoton na IMF da Bankin Duniya shi ne na cewar za a cimma manufar ta MDD na rage yawan masu fama da bala’in talauci da misalin kashi 50% nan da shekarar ta 2015, to amma fa wannan ci gaban zai samu ne a kasashen China da Indiya da suka fi kowa yawan jama’a a duniya. A sakamakon bunkasar tattalin arzikin da kasashen biyu ke samu daruruwan miliyoyi na al’ummoninsu zasu fita daga kangin talauci. Amma dangane da ragowar kasashe masu tasowa, ba za a samu wani ci gaba na a zo a gani ba, kamar yadda bankin duniya da asusun IMF suka nunar. Lamarin ya fi tsamari akan kasashen Afurka, inda rahoton ya ce za a samu karin 10% na yawan matalauta ‚yan rabbana ka wadata mu, a maimakon raguwar yawansu nan da shekara ta 2015. An saurara daga Zia Qureshi shugaban tawagar da ta rubuta rahoton na hadin guiwa tsakanin Bankin Duniya da Asusun IMF yana mai bayanin cewar ba za a samu wani canji na a zo a gani dangane da manufar da aka sa gaba ba muddin aka ci gaba da tafiya akan manufofin da ake kai na taimakon raya kasashe masu tasowa
Wajibi ne a samu karin taimako ga kasashe masu tasowa, sannan su kuma kasashen a nasu bangaren tilas ne su kawo canji ga manufofinsu. Wajibi ne su nemo wata nagartacciyar hanya ta aiwatar da kudaden taimakon a fannonin da suka dace. Kamata yayi a yi amfani da kudaden taimakon wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kyautata jin dadin rayuwar talakawan kasa ‚yan rabbana ka wadata mu. Bunkasa yawan kudaden taimakon kawai ba zai tsinana kome ba.
To sai dai kuma rahoton bai hada dukkan kasashen Afurka a karkashin laima daya ba, inda ya ware kasashe 12 da suka hada har da Ghana da Mali da Muzambik da Tanzaniya da kuma Uganda, wadanda a cikin shekaru goma da suka wuce suka rika samun bunkasar da ta kai ta kashi 5.5% ga tattalin arzikinsu. To sai dai kuma alkaluma na Bankin Duniya da asusun IMF sun ce za a bukaci bunkasa ta kashi 7% domin cimma burin da aka sa gaba na rage yawan masu fama da bala’in talauci da misalin kashi 50%. Babban abin da ya fi ci wa marubuta rahoton tuwo a kwarya shi ne mawuyacin halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya da harkar ilimi. A yayinda aka kiyasce cewar mutane miliyan 2 zasu yi asarar rayukansu a wannan shekarar sakamakon cutar Aids a nahiyar afurka, kazalika a daya bangaren akwai wasu yara miliyan 115 da basu da ikon halartar ajujuwan makarantun faramare a sassa daban-daban na nahiyar Afurka. Shawarar da rahoton ya bayar dai shi ne, kasashe masu tasowa a nasu bangaren su yi bakin kokarinsu wajen kyautata manufofinsu na kiwon lafiya da harkar ilimi, sannan su kuma kasashe masu ci gaban masana’antu su ribanya yawan kudadensu na taimako su kuma bude kofofin kasuwanninsu ga amfanin noma daga kasashe masu tasowa.