Sakamakon rahoton ENDSARS ya bar baya da kura
November 16, 2021A jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya kwamitin da gwamnati ta kafa kan zanga-zangar EndSars da ake zargin jami'an tsaro da wuce gona da iri ya gabatar da rahotonsa inda a ciki, aka nemi a biya diyya na kimanin Naira miliyan 410, ga mutane 70 da rikicin ya shafa.
A daya bangaren kuwa, Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, batun kisan masu zanga-zangar ta #EndSARS na kunshe cikin rahoton bincike da aka mikawa gwamnatin jahar Legas. Duk da cewa ba a fitar da rahoton ga jama'a ba, amma kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce masu binciken sun siffanta abin da sojojin suka yi a shekarar da ta gabata a matsayin kisan gilla da sunan tarwatsa masu zanga-zangar ta #EndSARS da masu fafutuka suka shirya a kan zargin cin zarafi da jami'an 'yan sandan rundunar SARS ke yi a kasar.
Kawo yanzu dai hukumar soja da ta 'yan sandan kasar ba su ce uffan ba kan wannan sabon rahoton, sai dai a baya sun sha nanata cewa ba su yi amfani da harsashi mai rai ba kan masu zanga-zanga. To amma masu rahoton sun ce sun ga alamun 'yan sanda sun yi kokarin boye wasu hujjojin irin tabargazar da jami'an tsaro suka yi a Lekki Toll Gate da ke Lagos inda aka yi wannan artabu.
Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun yi amfani da harsashi mai rai, yayin tarwatsa masu zanga-zangar #EndSARS a jahar Legas cikin shekarar da ta gabata ta 2020.