1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton UNESCO akan al'amuran Ilimi a 2005

February 2, 2005

A baya-bayan nan ne kungiyar UNESCO ta gabatar da rahotonta akan al'amuran ilimi a shekara ta 2005 a ma'aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus

https://p.dw.com/p/BvdN

Ilimi dai wani bangare ne na hakkin dan-Adam. A sakamakon haka a lokacin taron duniya akan ilimi da aka gudanar a Dakar fadar mulkin kasar Senegal a shekara ta 2000 dukkan mahalarta taron daga kasashe 164 suka lashi takobin cimma wasu manufofi shida game da al’amuran ilimi nan da shekara ta 2015. Daga cikin wadannan manufofi har da ba da ilimi kyauta ga kowa-da-kowa da kamanta adalci a manhajar ilimi. Rahoton na kungiyar ilimi da al’adu ta MDD mai taken "Al’amuran ilimi dangane da shekara ta 2005", yayi bitar sakamakon da aka cimma a game da wadannan manufofin da aka gabatar tun a shekara ta 2000. Shin wadannan abubuwa ne aka cimmusu kuma a ina ake fama da gibi domin kai wa ga wa’adin na shekara ta 2015? Steve Packer mataimakin shugaban tawagar da ta gabatar da ta rubuta rahoton na UNESCO yayi nuni da dimbim yawan mutanen da ba su iya rubutu da karatu ba, wadanda har yau ake ci gaba da fama da su, musamman a wasu daidaikun kasashe, inda ya ce daga cikin mutane kimanin miliyan dari takwas da ba su san ko-bihim ba, akwai wasu kashi 70% daga kasashe tara, inda kasar Indiya ke da kashi 34% daga cikinsu. Kazalika a cikin rahoton na bana, ko da yake an nuna samun ci gaba dangane da yawan yara dake da damar halartar ajujuwa abin da ya hada har da ‚yan mata, amma fa ana fama da tafiyar hawaniya a wannan bangaren. Alkaluma sun nuna cewar kimanin yara miliyan dari ne ba su da ikon halartar ajujuwan makarantu a sassan duniya dabam-dabam. A wasu kasashen ana fama da karancin litattafai da sauran kayayyakin makartantu sakamakon bunkasar da aka samu na yawan almajirai da kan cika makil a ajujuwa. Kazalika ana fama da karancin kwararrun malamai, lamarin da ya sanya rahoton UNESCO din na bana ya fi mayar da hankali ga ingancin al’amuran ilimin a kasashen da dama. A yayinda kasa kamar Masar take bakin kokarinta wajen inganta al’amuran ilimi a makarantun kasar, akwai wasu kasashen kamar Sri Lanka dake ci gaba da lalube a cikin dufu domin nemo bakin zaren warware matsalar koma bayan ilimin da tayi shekara da shekaru tana fama da ita. Muhimmin abin da ake bukata wajen daga matsayin ilimi shi ne kwararrun malamai da kananan ajujuwa wadanda ba su da cunkoson almajirai a cewar Steve Packer, mataimakin tawagar kwararrun da kungiyar UNESCO ta dora musu alhakin gabatar da rahoton na bana. Ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus ta kan ba da gudummawa mai tsoka wajen tallafa wa tawagar kwararrun da UNESCO kan nada domin nazari da gabatar da rahotonta mai taken: "Ilimi ga kowa-da-kowa" a duk shekara.