1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da China sun yi adawa da kai Siriya kotu

May 22, 2014

Wannan dai shi ne karo na hudu da kasashen biyu suka yi amfani da matsayinsu na masu zaunanniyar kujera wajen hawa kujerar na ki a kan rikicin na Siriya.

https://p.dw.com/p/1C4rI
UN Sicherheitsrat Resolution Syrien 22.5.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasashen Rasha da China sun hau kujerar na ki a dangane da kudurin komitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, na gabatar da rigingimun Siriya a gaban kotun kasa da kasa domin binciken yiwuwar aikata laifukan yaki.Wannan matsayi na kasashen biyu dai ya yi karo da martanin bacin rai daga wadanda suka dauki nauyin gabatar da kudurin.

Wannan dai shi ne karo na hudu da Rasha da China suka yi amfani da matsayinsu na masu zaunanniyar kujera a komitin sulhun, wajen hawa kujerar na ki dangane da daukar tsauraran matakai kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Siriya. Sauran wakilai 13 na komitin sulhun sun kada kuri'ar amincewa da wannan kuduri.

Sama da kasashe 60 na majalisar ne dai, suka bada goyon bayansu kan shirin kudurin da Faransa ta gabatar, wanda ke nuna goyon bayan kasashen duniya kan tabbatar da adalci a rikicin daya tilasta miliyoyin mutane tserewa daga matsugunnensu, bayan lamushe rayukan mutane sama da dubu 160, kamar yadda masu fafutuka suka nunar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu