Rasha ta yi na'am da tayin sulhu da 'yan adawar Siriya suka yi
February 21, 2013Gwamnatin Rasha tare da kungiyar kasashen Larabawa sun bukaci gwamnatin Siriya ta amince da tayin zama kan teburin shawarar da 'yan adawar kasar suka gabatar mata, kana ta kulla yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi na kusan shekaru biyu kenan. A lokacin daya ke jawabi a wannan Larabar, sakatare janar na kungiyar kasashen Larabawa Nabil al-Arabi ya shaidawa Rasha irin nauyin daya rataya a wuyanta, na bukatar yin anfani da karfin fada-ajin da ta ke da shi akan Siriya, domin taimakawa shawo kan rigingimun da kasar ke fama da shi. Ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya bayyana cewar a shirye yake ya karbi bakuncin duk wani taron da zai gudana a tsakanin shugaba Bashar al-Assad na Siriya da kuma wakilan 'yan adawar kasar, amma ya jaddada cewar babu alamar matakin soji ne kawai zai warware rikicin.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu