1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da fargaba kan halin da Boris Johnson ke ciki

Abdoulaye Mamane Amadou
April 7, 2020

Ana ci gaba da nuna fargaba dangane da halin da firaministan Birtaniya Boris Johnson yake ciki a asibiti biyo bayan kamuwa da cutar numfashi ta Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aZKV
Boris Johnson Premierminister Großbritannien
Hoto: Imago Images/PA Images/S. Dawson

Tuni fadar gwamnatin kasar ta sanar da sarauniyar Ingila halin da Boris Johnson ya ke ciki, kana kuma ta bayyana matakin nada Dominic Raab ministan harkokin wajen kasar, a matsayin wanda zai wakilci firaministan a duk inda bukatar kasancewarsa ta taso.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai rahotanni suka ce firaminista Boris Jonhson ya nufi asibiti don kara kula da lafiyarsa, lamarin da ya kara tsananta a yammacin jiya. Shugaban Amirka Donald Trump da na Faransa Emmanuel Macron da firaminsitan kasar Italiya Giuseppe Conte, duk sun nuna damuwa kan tsanantar rashin lafiyar ta Boris Johnson, tare da yi masa fatan samun sauki.