May 13, 2017
Bari mu fara da jaridar Der Tagesspiegel wadda ta yi sharhi kan kasar Somaliya. Jaridar ta fara ne da ruwaito sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson na cewa dole ne a karfafa dan kwaryakwaryar zaman lafiyar da aka samu yanzu a Somaliya, matukar ba so a ke kasar ta sake zama barazana ga duniya ba. Jaridar ta ce yayin da 'yan shekarun bayan gwamnatin Somaliya ta kasa zama a kasar, gwamnatin da ke ci yanzu ta koma kasar inda ta fara aikin sake gina kasar daga kurfai. Sai dai duk da wannan ci gaba da aka samu bayan shekaru gommai na yake-yake, har yanzu da jan aiki gaba, domin baya ga matsalar tsaron Somaliya na fama da matalsar fari da karancin abinci. Saboda haka taron tallafa wa kasar da Birtaniya ta dauki nauyinsa kamar faduwa ce ta zo daidai da zama. Fata dai shi ne za a cika alkawuran da aka dauka.
Gano 'yan matan makarantar Chibok
A karshe an samu 'yanci inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai mayar da hankali a kan sako wani kaso na 'yan matan Chibok da Boko Haram ta yi garkuwa da su tun a watan Afrilun 2014.
Jaridar ta ce shekaru uku da suka gabata kungiyar 'yan ta'addan ta Boko Haram ta sace 'yan mata 'yan mata makarantar Sakandaren Chibok kusan 280, yanzu an sako karin 82 da aka yi musayarsu da wasu kwamandojin kungiyar, sannan a na ci gaba da tattaunawa da zumar sako sauran 'yan matan da ake garkuwa da su. Ko da yake sun samu 'yancinsu amma har yanzu ba su koma gida wajen iyaye da sauran dangi ba. A watan Oktoban 2016 an sako wasu 21 su din ma ana korafin cewa an kebe su daga bainar jama'a. Duk da haka dai godiya da kuma yabo ga gwamnatin Muhammadu Buhari da take bada muhimmanci ga kokarin sako wadanda Boko Haram ke garkuwa. Kamata ya yi gwamnati ta fadada wannan kokarin yadda za a iya kubutar da dukkan mutanen da ke hannun Boko Haram.
Lafiyar Shugaba Buhari
Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci kan rashin lafiyar Shugaba Buhari tana mai cewa tun wasu watanni ke nan shugaban na Najeriya mai shekaru 74 wanda ke kuma mafi yawan 'yan Najeriya suka dora kyakyawan fata kanshi, yake fama da rashin lafiya. A ranar Lahadi jim kadan bayan ya karbi bakoncin 'yan matan Chibok 82 da suka samu 'yancinsu daga Boko Haram, a karo na biyu cikin wannan shekarar shugaban ya tafi birnin London don duba lafiyarsa. Jaridar ta ce rashin lafiyar shugaban ya zo wa Najeriya mai fama da rikice-rikice, a wani lokaci da bai dace ba.