Rashin tabbas kan taron Siriya
October 21, 2013Talla
Akwai rashin tabbas kan gudanar da taro neman kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Siriya. Yayin da kungiyar Kasashen Larabawa ke cewa za a gudanar da taron cikin watan gobe na Nowamba, mai shiga tsakani kan rikicin a madadin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa Lakhdar Brahimi ya ce, babu ranar da aka saka na taron da zai guda a birnin Geneva na kasar Switzerland.
A kasar ta Siriya dai, wani harin kunar bakin wake da aka kai da babbar motar daukan kaya ya yi sanadiyar hallaka mutane 30, sannan wasu masu yawa suka samu raunika a garin Hama.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal