1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas na samun tallafin Amirka

April 4, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan matakin Amirka na zabtare kudaden taimakon raya kasashe na hukumar majalisar mai kula da yaduwar al'umma.

https://p.dw.com/p/2aguc
Somalia Flüchtlingslager in Doolow
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi kan zabtare kudaden taimakon raya kasashe da gwamnatin Amirka karkashin Shugaba Donald Trump ta yi, abin da ya hada da kudin hukumar majalisar mai kula da yaduwar al'umma. Guterres ya ce lamarin zai haifar da mummunar illa ga mata da yara a kasashen duniya.

Babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin Amirka na yanke kudaden da take bai wa hukumar zai kawo tarnaki game da lafiyar mata da yara mata cikin kasashen na duniya.

Karkashin sabon shirin na Amirka a zabtare kimanin dala milyan 32 da rabi daga kudaden kasafin kudin shekara ta 2017 da hukumar za ta samu daga Amirka, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasra ta Amirka ta tabbatar. Kuma babu tabbaci kan samun sauran daukacin kudaden da hukumar Majalisar Dinkin Duniyar mai kula da yaduwar al'umma daga gwamnatin ta Amirka.