Rashin tsaro na mummunan tasiri kan noma a Filato
July 21, 2023Manoma da ke shiyyar tsakiyar Filato na ci gaba da zaman fargaba biyo bayan yawan hare-haren 'yan bindiga da ya samo asali daga rikicin makiyaya da manoma, lamarin da ya yi sanadiyar rayuka da dimbin dukiyoyi a karamar hukumar Mangu. Ya zuwa yanzu rundunar sojin Najeriya ta tura jami'anta inda suka kafa sansanoni a yankin, amma har zuwa manoma na tsorace a cewar Rabecca Simon
Tun cikin watan Mayun 2023 ne aka soma fuskantar rikici a Mangu, yankin da ya yi fice wajen noman dankalin Turawa da masara. A lokutan baya, 'yan kasuwa daga wajen jihar Filato kan yi jigilar anfanin gona zuwa kasuwannin wasu jihohi Najeriya da ma kasashen ketare. Sai dai a yanzu, baya ga matsalar tsaro manoman yankin na fama da karancin kayyayakin aikin gona, a cewar Geman Alex, wani fittacen manomi.
Karamar hukumar Bokkos ma ta sha fama da matsala ta rashin tsaro. Talatu Zakka da ta yi fice a noman dankalin Turawa ta ce tun ba yau ba suke fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga. Shi kuwa shugaban kungiyar manoman jihar Filato John Chindap Wuyep ya ce hanya guda da za'a rage radadin karanacin abinci a kakar bana shi ne kara daukan matakan tsaro tare da bunkasa noman rani .
Yanzu haka dai, hare-haren 'yan bindiga sun sanya daruruwan manoma guje wa gonakinsu, yayin da wasu da rikicin ya raba wasu da dama daga muhallansu. Jama'a na fatan hukumomi za su kara azama wajen magance wannan matsala ta tsaro.