1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar sojojin Masar a harkokin mulkin kasar

July 3, 2013

Sojojin Masar sun aiwatar da barazanar da suka yi a kan gwamnatin Mursi kwanaki biyu bayan wa'adin da suka diba. Sai dai wasu 'yan kasar na adawa da babakeren sojoji a harkokin mulki..

https://p.dw.com/p/191KC
Hoto: picture-alliance/landov

Wadanda ke adawa da manufofin shugaban na Masar ne suka bukaci sojoji sun rabasu da abin da suka kira mulkin fir'aunanci na Mohammed Mursi da kuma na kungiyarsa ta 'yan uwa musulmi. Su kuwa sojojin ba su kasa a guywa ba wajen amsa kirar da masu zanga-zanga suka yi, inda suka bukaci Mursi ya warware rikicin da Masar ke fama da shi kan nan da yammacin wannan laraba. Hakazalika sun yi barazanar amfani da karfin fada a jinsu wajen kawo karshen sa toka-sa-katsi da ke tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna.

Da ma tun a ranar lahadi sojojin na Masar sun nuna alamun cewa suna bayan masu zanga-.zangar kin jinin gwamnati, inda suka yi ta kasa-kasa da jiragen masu saukar angula wadanda suka daura wa tutar ta Masar a lokacin da suka yi ta shawagi a dandalin Tahrir. Maha Azzam da ke zama jami'ia a cibiyar Chatam House ta Birtaniya, ta ce duk da cewa masu zanga-zanga sun nuna doki game da goyon bayan sojoji, amma ba wai ya na nufin cewa suna so sojojin sun yi juyin muki ba ne.

Ägypten Proteste gegen Mursi Kairo 03.07.2013
'yan adawa da magoya bayan Mursi ke zanga-zangaHoto: Reuters

"Wani bangare na al'uma ya san karfin fada a ji da sojoji ke shi. Amma ba wai suna so a yi juyin mulki ba ne. A daura da haka ma dai sun nemi sojojin sun tilasta wa shugaban kasa mutunta hakkokinsu. Wannan amsar farkon ake jira daga Mursi-wanda ke zaman Zababben shugaban farko a Masar."

Ägypten Proteste Militär
Sojoji sun goyi bayan masu zanga-zangar adawa a MasarHoto: Getty Images

Sojoji sun saba taka rawa a harkokin mulki

Ko da shi ke dai sojojin na yi wa Mursi biyeyya a matsayin shugaban rundunar sojojin Masar, amma kuma sun saba yin ruwa da tsaki a al'muran mulki. Tun dai lokacin da Janar Gamal Abdel Nasser ya shugabancin kasar tsakanin shekarar 1952 zuwa 1970 ne, sojojin suka samu gindin zama a Masar. A zamanin Hosni Mubarak ma dai sun ci-gaba da cin karensu ba tare da babbaka. sai dai daga bisani bayan da guguwar neman sauyi ta yi awan gaba kujerar dan kama-karyan, an kasa fassara rawar da sojojin suka yi niyar takawa lokacin da suka yi rikon kwarya.

Da yawa daga cikin 'yan Masar sun zarge su da yunkurin kakkange madafun iko, maimakon neman dora kasar kan turbar demokaradiya. A wannan lokaci dai sojojin sun yi burus da duk wata suka da 'yan kasar ke yi musu game da salonsu na mulki. Sai dai maimaikon haka, sun lakada wa wani matashi dan karen duka a dandalin Tahrir bayan da ya fito ya soki lamirinsu, ko ya ke daga bisani sun nemi gafara. Annette Ranko ta cibiyar GIGA da ke Hamburg na Jamus ta ne sojojin na masar na da babban tabo a jikinsu.

Ägypten Symbolbild Mohammed Mursi
Mursi ne zababben shugaba na farko a MasarHoto: OZAN KOSE/AFP/Getty Images

"Ka da a manta cewa shekaru biyu da rabi a suka gabata wato bayan hambarar da Mubarak, sojoji ne suka yi rikon kwarya. A wannan lokaci dai sojojin sun yi wasu 'yan Masar ba daidai ba. saboda haka ne wasu suka nuna fargabar cewa ba za su sauka daga kujerar mulki ba."

Shi dai shugaban na Masar bai nuna alamun mutunta wa'adin na sojoji ba. Amma kuma ya gana so da dama da bangaren na adawa da kuma manyan jami'an Masar da ke kula da harkokin tsaro, da nufin samun maslaha a rikicin da ya gurganta kasar ta Masar.

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu