1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya ki amincewa da zaman lafiya

Mouhamadou Awal Balarabe
August 28, 2018

Shugaban 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka tanada da gwamnati da nufin kawo karshen yakin basasa da kasar ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/33tfl
Äthiopien | Südsudanesischer Rebellenführer Riek Machar trifft Präsidenten des Südsudan Salva Kiir
Hoto: Reuters/T. Negeri

Ministan harkokin wajen Sudan da ke shiga tsakanin Al-Dirdiry Ahmed ya ce Kungiyoyin 'yan adawa na Sudan ta kudu ciki har da SPLM-IO ta Riek Machar sun ki sa hannu a kan takardar saboda ba a yi la'akari da wasu sharudansu ba. Alhali a ranar 5 ga watan Agusta, shugaban kasar Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar sun sanya hannu kan wata yarjejeniya, wacce ta tanadi komawar Machar gida domin ya rike daya daga cikin manyan mukamai na mataimakin shugaban kasa.

Sai dai masu shiga tsakani na Sudan suka ce  za su mika wannan takarda ga kungiyar kasashen gabashin Afirka da suke shafe tsawon watanni na aiki don sake farfado da zaman lafiya a Sudan ta kudu. Dubban mutune sun rasa rayukansu a Sudan ta Kudu, yayin da kimanin mutane miliyan 4  suka kaurace wa matsugunansu tun bayan barkewar tashin hankali a watan Disemban 2013, shekaru biyu bayan da ta samun 'yancin kanta.