1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadin likitoci a kan cutar Coronavirus

Abdourahamane Hassane
February 28, 2020

Shirin kiwon lafiya na wannan mako na Lafiya Jari ya duba irin matakan kariya da a kan iya dauka na riga kafin kamuwa da cutar Coronavirus, musammun ma ga matafiya daga Afirka zuwa sauran kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/3YbCI
Coronavirus in Deutschland Touristin aus Asien in Düsseldorf
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Meissner

Cutar Coronavirus wacce ake kira da sunan Mers kwayoyin cuta na numfashi an fara ganota ne a shekara ta 2012 a Saudiyya, wanda a lokacin ta bazu a cikin kasashe 27. Kafin a baya-baya nan ta yi mummunar barna a China inda sama da mutum dubu suka rasa rayukansu, yayin da ta bulla a Italiya da Faransa da Jamus da ma Najeriya. Cutar tana daga cikin rukunin kwayoyin cuta na numfashi kamar SAS wacce kafin ta yadu ga dabobi ta bazu a cikin sahun tsuntsaye irinsu jemage. Likitoci na yin gargadin cewar babban riga kafi na kamuwa da cutar shi ne kula da wanke hannu da kuma saka takunkumi na kare fuska. Cutar tana da alamu iri daya da murar sai dai a cikin lokaci guda tana iya yin muni ta kai ga yin kisa don haka likitoci na yin gargadi ga matafiya, idan an je an dawo a rika yin gwaji na kiwon lafiya. Masu kiwon dabobi da jami'an da ke aiki a mayakan ya zama wajibi su rika yin hattara wajen daukar matakan riga kafi a cewar likitocin.