Rikici a Pakistan
November 5, 2007Jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da barkonon tsohuwa,sunyi arangama da ayarin lauyoyi dake zangazangar nuna adawa da dakoar ta baci da shugaba General Pervez Musharraf ya kafa tun ranar asabar a wannan kasa.
Kasar ta Pakistan ta fada wannan rikici nedai, adai dai lokacin da kasashen duniya da kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin jama’a ke cigba da bayyana adawarsu,adangane da wannan doka da gwamnatin ta kafa,wanda kawo yanzu ya haddasa kulle sama da mutane 1,500 a gidajen yari.
A ranar asabar data gabata nan nedai Musharraf ya dakatar da kundun tsarin mulkin kasar,gabannin zartarwar kotun koli adangane da sakamakon zaben sa.Kazalika ya kuma kori Alkalai masu ‘yancin kai ,tare da bawa wasu ikon cigaba da tafiyar da lamuran kasar.
A yau din dai shugaba Musharraf ya gana da jakadun kasashen ketare da ke Pakistan,inda ya shaida musu cewar sashin sharia’ar wannan kasa na kawo koma baya ,dangane da kokarin yakar tarzoma da ake tafiyarwa.
Masu wannan gamgamin dai na cigaba da kokawa dangane da yadda ake take hakkokin jama’a ba tare da damar basu daman fadin albarkacin bakinsu ba kamar yadda daya daga cikinmasu fafutukar kare hakkin jama’a dake Islamabad Tahira Abdullah ta shaidar..
“An haramta mana gudanarwa da kowane irin taro,bamu da damar tofa albarkacin bakinmu ,kana ba mu da damar yin hulda da juna”
To sai dai wa wani Ɗan kasar wannan itace hanya daya da zaa iya shawo kan karuwar matsalolin da pakistan ke fuskanta...
“A kowa ce rana wannan kasa tana dada tsunduma cikin hali mawuyaci na tashe tashen hankula,adangane da hakane na ke ganin cewar wannan dokar ta baci itace zabin karshi.”
Shugabar kungiyar kare hakkin bil adama ta Majalisar Ɗunkin Duniya Louise Arbour,ta bayyana rashin jin dadinta a dangane da wannan dokar ta Ɓaci ta aka kafa a Pakistan,tare da cigaban tsare Alkalai da Lauyoyin kasar a gidajen yari.
A kusan dukkan biranen kasar ta Pakistan dai ana cigaba da arangama tsakanin jami’an ‘yan sanda da lauyoyi da kuma alkalan dake wannan zanga zangar,wanda yayi sanadiyyar munanan raunuka,baya ga Ɗumbinsu dake tsare.
A Ɓangarensa premier Shaukat Aziz na pakisatan din yace dukannan waɗɗannan matakai anyisu ne domin ceto Al’ummar wannan kasa...
“Mun dauki dukkan waɗannan matakai ne da nufin samrda da haɗin kan kasa da zaman lafiya,tare da tabbatar da cewar gwamnati na ta tafiyar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba,kuma yin hakan zai haifar da Ɗa mai idanu.”
To sai wa manyan masu adaw da Musharraf kuma tsoffin shugabbanin gwamnatocin kasar Benezir Bhuto da Nawaz Sharif ,wannan dokar ta Ɓaci da aka kafa ya saɓawa kundun tsarin mulkin kasa.Kuma a kullum Musharrfaf yana ikirarin sahihiyar demokradiyya.Shahbaz Sharif dai Ɗan uwan tshohon premier Nawaz Sharif ne...
“Alokacin daya kifar da gwamnati a ranar 12 ga watan Oktoba 1999,Musharraf ya rantsewa al’ummar wannan kasa cewar zai sauya demokradiyyar abun kunya da,sahihiyar Demokradiyya,amma a yau ina ake”.