Rikici na ci gaba a Sudan ta Kudu
April 25, 2018Talla
'Yan adawar dai sun bayyana saukar ta Salva Kiir a matsayin wani bangare na kawo karshen yakin basasar da kasar ta kwashe tsahon shekaru hudu tana fama da shi. Kiir ya yi zargin cewa masu adawa da gwamnatinsa ne kawai ke kawo wasu bukatu da basu da tushe balle makama. An dai yi ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin basasar da ya barke tun a shekara ta 2013, sai dai tun ba a je ko ina ba yarjejeniyar ke rushewa a jaririyar kasar ta duniya.