1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin China da Japan na ci gaba

October 2, 2012

Jiragen ruwan China hudu sun kutsa tsibiran nan da suke takaddama da Japan akai. Fadar mulki ta Tokyo ta nemu direbobin da su wuce tun suna mutunta juna.

https://p.dw.com/p/16IXZ
A Japan Coast Guard patrol boat sprays water against a Taiwanese fishing boat, top, near disputed islands, called Senkaku in Japan and Diaoyu in China, in the East China Sea, Tuesday, Sept. 25, 2012. Japanese coast guard ships fired water cannon to push back Taiwanese vessels Tuesday in the latest confrontation over a group of the tiny islands, as the main contenders, China and Japan, opened talks in a diplomatic effort to tamp down tensions. (AP Photo/Kyodo News) JAPAN OUT, MANDATORY CREDIT, NO LICENSING IN CHINA, FRANCE, HONG KONG, JAPAN AND SOUTH KOREA
Hoto: AP Photo/Kyodo News

Hukumomin Japan sun bayyana cewa jiragen ruwa hudu mallakar gwamnatin China sun kutsa tsibiran nan biyu da suke takkadama akai. Fadar mulki ta Tokyo ta ce tuni ta bukaci matukan jiragen na ruwa da su wuce daga tsibiran biyu saboda mallakar kasar Japan ne. Tun dai bayan da Japan ta ayyana tsibiran Senkaku a matsayin wani bangare na kasarta aka fara sa toka sa katsi tsakanin makobtan biyu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da China ta keta shingen ruwa da ke tsakaninta da Japan ba. Hakazalika 'yan kasarta sun shafe kwanaki suna gudanar da zangar zangar yin Allah wadai da abin da suka kira yunkurin Japan na kwace musu wani bangare na kasarsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh