1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin gwamnan CBN da 'yan siyasa

December 20, 2022

Yayin da ake ci gaba da takaddama kan sabbin manufofin kudi a Najeriya, alamu na nuna shirin raba gari tsakanin gwamnan babban bankin kasar da manyan 'yan siyasar da ke zarginsa daukar nauyin harkokin ta'addanci a kasar.

https://p.dw.com/p/4LFK9
Sabbin takardun kudin Naira na Najeriya
Sabbin takardun kudin Naira na NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

A yayin da wutar rikici ke ta kara ruruwa a tsakanin gwamnan babban bankin tarrayar Najeriya da 'yan siyasa, a waje guda kotunan kasar na neman kauce wa rikicin da ke rikidewa ya zuwa batu na ta'adda.

Masu siyasar da ke fuskantar zabe dai basu boye adawarsu ba bisa manufar babban bankin na daukar kasar zuwa tsarin kudi na zamani. To sai dai kuma wani yunkuri a bangaren hukumar DSS ta farin kaya da ke neman izinin wata kotu na kame gwamnan dai daga dukkan alamu na fuskantar koma baya.

DSS din dai na zargin gwamnan da ta'ammali da kudaden ta'adda a wani abin da ke zaman ba sabonba, da kuma ke neman daukar rikicin zuwa sabon matsayi. Dr yahuza Getso dai na sharhi bisa batun tsaro da kuma yace matakin na jami'an tsaron farin kaya na da babban burin mai da gwamnan zuwa ga hayyaci bayan tsayuwar gwamin jaki bisa sabbin manufofin kudin.
Tun kafin sabon zargin dai dama gwamnan ya fuskanci jerin kamfen din neman sai ya kauce, daga masu tunanin akwai sauran sake bisa ga yadda tsarin kudin ke neman sauyawa.

Öl Globaler Einfluss Geld Finanzen Nigeria Naira
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Har ya zuwa yanzu dai alal misali ana muhawara bisa wasu jerin zargi da wani dan majalisar kasar ke cewa gwamnan ya jagoranci wasoso da wasu kudaden da suka kai triliyan 89 ko kuma kasafin kudin kasar na shekaru kusan biyar. Nasarar sallamar Emefiele dai za ta maida shi gwamnan babban bankin na biyu a jere da masu siyasar kasar suka tilasta wa barin mulki bisa banbancin manufofi.
A shekara ta 2014 ne dai tsohuwar gwamnatin kasar ta dakatar da Sunusi lamido Sunusi daga kujerar gwamnan bayan wani zargin batan dabo na wasu dubban miliyoyin daloli. Abubakar Ali na zaman kwararre kan tattalin arziki da kuma yace rigingimun da ke faruwa a cikin kasar na iya jawo matsala ga tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal.

Ginin Babban bankin Najeriya
Ginin Babban bankin Najeriya

Rahotannin da ke fitowa daga sassa daban daban a tarrayar Najeiryar dai na nuna 'yan siyasa na wasoson sabbabin kudaden tare da boye su domin harkar zaben na badi. Abin kuma da ya jawo mummunan karancin sabbin kudaden a zauren hada hada na bankuna.