1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin kabilu a arewacin kasar Kenya.

May 6, 2015

Rahotanni daga birnin Nairobi na kasar Kenya na cewa, a kalla mutane 75 aka kashe cikin kwanaki hudu, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kabilu arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/1FLCG
Bildergalerie Turkana Stamm aus Kenia
Hoto: Reuters/Goran Tomasevic

Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban kungiyar agaji ta Red Cross na kasar ta Kenya Abbas Gullet, ya ce bai kamata ba a wannan lokaci cikin karni na 21, a ce al'ummomin yanki guda suna hallaka kanunsu irin haka. Ana zargin 'yan kabilar Turkana ne da kai hari kan 'yan kabilar Pokot inda harin na farko ya yi sanadiyar rasuwar mutane 54 daga bengarorin biyu cikinsu mata biyar da kananan yara hudu.

A cikin kwana na hudu na wannan rikici, adadin wadanda aka kashen ya kai na mutun 75. Fadan ya barke ne sakamakon wani samame da 'yan kabilar Pokot suka kai a garuruwan 'yan kabilar Turkana, inda suka sace musu daruruwan awaki. Kawo yanzu dai a kalla mutane 350 ne suka bar matsugunnansu sakamakon rikicin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu waba